1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Saliyo: Koroma da ke daurin talala zai fita waje

January 18, 2024

Saliyo ta amince wa tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma tafiya kasar waje domin neman magani duk da tuhumar da ake masa na hannu a yunkurin juyin mulkin ranar 26 ga watan nuwambar 2023 a birnin Freetown.

Tsohon Shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma
Tsohon Shugaban Saliyo Ernest Bai KoromaHoto: Murtala Kamara/DW

Lauyan tsohon Shugaban, Joseph Fitzgerald Kamara ya ce kotu ta yarje wa Koroma tafiya zuwa Najeriya domin neman magani a cutar da hukumomin ba su yi cikakken bayani a kai ba.

Tun da fari dai an shirya cewa tsohon shugaba Ernest Bai Koroma zai bayyana a gaban kotun Saliyo a jiya Laraba, to amma aka dage zaman kotun zuwa 6 ga watan Maris na wannan shekara.

Ernest Bai Koroma, wanda ya mulki kasar ta Saliyo daga 2007 zuwa 2018 na fuskantar tuhuma kan zargin cin amanar kasa da wasu laifukan na daban na yunkurin kifar da gwamnatin kasar a watan Nuwambar bara.

Yunkurin juyin mulkin na Saliyo ya haifar da rudani a kasashen yammacin Afrika na guguwar juyin mulki da tuni kasashe irin su Mali da Burkina Faso da Jamhuriyyar Nijar da Guinea suka fuskanci juyin mulki.