1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Saliyo: Kotu ta ba da umarnin cafke jagoran adawar kasar

December 14, 2023

Wata kotu a Saliyo ta bada umarnin kama babban jagoran adawa a kasar kuma wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar na watan Yuni, Samura Kamara, sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Jagoran adawar Saliyo, Samura Kamara
Hoto: John Wessels/AFP/Getty Images

Wata kotu a Saliyo ta bada umarnin kama babban jagoran adawa a kasar kuma wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar na watan Yuni, 2023, Samura Kamara, sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Kotun daukaka kasar Saliyo dai ta same shi da laifin sayar da hannun jarin kamfani sarrafa ma'adinai a shekara ta 2012, a lokacin da yake ministan kudi zamanin gwamnatin shugaba Ernest Bai Koroma.

Duk da kawo yanzu dai lauyoyin Kamara basu ce uffan ba dangane da wannan sammaci.

Kamara dai shi ne ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da ya gabata, bayan hukumar zaben kasar ta Saliyo ta sanar da shugaba Julius Maada Bio, a matsayin wanda ya lashe zaben, sakamakon da Kamaran ya yi watsi da shi.

Galibin mambobin jam'iyyar APC ta Koroma da Kamara ya yi mata takara na fuskantar tuhume-tuhume da suka bayyana a matsayin bita-da-kulli.