1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sallar Idi ta gudana cikin lumana a Najeriya da Nijar

Abdul-raheem Hassan MNA
September 1, 2017

An gudanar da Sallar Idi lami lafiya a dukkanin sassan Arewa maso Gabashin Najeriya cikin tsauraran matakan tsaro, musamman a jihohin Borno da Yobe da a baya ke zama cikin fargabar mayakan Boko Haram.

Nigeria Maiduguri Moslems beten
Dimbin al'umma ke halartar SallahHoto: Reuters/Stringer

Jami'an tsaro sun takaita amfani da ababan hawa a jihohin Borno da Yobe har sai bayan da aka sauko daga Sallah Idi, kusan dukkanin wadan da suka halarci sallar sun yi ado kuma da ganin su suna cikin annashuwa saboda samun damar yin sallar ba tare da fargaba ba.

A dukkanin masallatan idin da ake Maiduguri an yi Sallah Idin lami lafiya da ma sauran wuraren da ke makobtaka da birnin. Haka labarin ya ke a jihar Yobe wanda ke zama jiha ta biyu da ta fi fuskantar kalubalen tsaro da hare-haren kungiyar Boko Haram, kuma jami'a sun yi biyayya da dokokin suka je masallatan Idi da kafa.

Jami'an tsaro ke gudanar da bincike a filin IdiHoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Baya ga takaita zirga-zirgan ababen hawa a loakcin gabatar da sallar Idi na bana, wasu al'umma ne suka bayyana yadda sallah ta riskesu cikin matsin tattalin arziki. Kananan yara ma ba'a barsu a baya ba inda suka ce sun samu shiga wuraren sallah Idi bana sabanin ta bara da ake turereniya da cunkoso da ta kai ga take wasu yara. Jama'a na ci gaba da hidimar yanka dabbobi da soye-soyen nama inda ake iya ganin jama'a yara da manya suna rabon nama kamar yadda aka saba.

A Jamhuriyar Nijar a wannan Asabar aka gudanar da babbar Sallar, bisa sanya ranar Sallah ta kasance ranar uku ga watan Satumba da majalisar koli ta Musulunci a kasar da ta yi.

Wakilinmu a Damagaram Larwanan Malam Hami ya ce komai ya tafi lafiya lau, a filayen Idin wannan yanki, inda suka yi cikan kwari. Sai dai wasu daga cikin al'umma sun ce layyar bana ba da su ba, saboda rashin na gwamna masu gida rana.