Salon shugabancin sabon jagoran Taliban
November 7, 2013'Yan Taliban na kasar Pakistan sun nada wanda ake zargi da kai wa Malalah Yousafzai hari wato Mollah Fazlullah a matsayin sabon shugaban kungiyarsu. Ana dangantashi da wanda ya saba amfani da kafar rediyo wajen yin zafafan hudubobi da kuma kwarewa a fannin gagwarmaya da makamai. Sannan kuma shi Mollah Fazlullah ne ya kafa shari'ar Musulunci daga shekara ta 2007 zuwa ta 2009 a tuddan Swat.
Sai dai kuma Mollah Fazlullah ya sa kafa ya yi fatali da tattaunawar samar da zaman lafiya da ake shirin yi tsakanin gwamnati da masu tsattsauran ra'ayin Islama. Kakakin Fazlullah ya bayyana wa manema labarai cewar, gwamnatin Pakistan da ke ci a yanzu ba ta da hurumin tattaunawa dasu saboda haramtacciya ce. Wannan ya zo ne kasa da mako guda bayan da Amirka ta yi amfani da jirgin da ke sarrafa kansa da kansa wajen kashe tsohon jagoran Taliban a Pakistan wato Hakkimullah Mehsud.
Gwamnatin ta Pakistan ta na kokarin shawo kan kungiyar Taliban da ta ajiye makamai domin kawo karshen rikicin da ya daidaita kasar da ta kunshi mutane miliyan 180.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Saleh Umar Saleh