1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salwantar rayuka a harin kudancin Yemen

August 5, 2012

Mutane 42 sun rasa rayukansu yayin da 37 suka jikata a wani harin bam da aka kai a lardin Abyan da ke kudancin Yemen lokacin jana'Izar wani sojan sa kai da kabilun kasar.

Wounded army soldiers are taken away from the scene of a suicide bombing near the southern Yemeni city of Zinjibar, capital of the Abyan province March 4, 2012. Suicide bombers linked to al Qaeda killed at least seven soldiers in coordinated attacks on military outposts in southern Yemen on Sunday, officials and residents said, part of an escalation of violence since a presidential vote two weeks ago. REUTERS/Stringer (YEMEN - Tags: POLITICS CRIME LAW MILITARY) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar a wani gari da ke cikin lardin Abyan na kudancin Yemen ya haddasa asarar rayukan mutane 42 tare da jikata wasu sama da 37. Hukumomin birnin Sana'a suka ce wannan harin ya faru ne lokacin jana'izar wani mutum da ke da alaka da sojojin sa kai, da suka taimaka wa dakarun gwamnatin yaki da ayyukan ta'addci na kungiyar Al-Qa'ida.

Ana dai danganta wannan danyen aikin da ramuwar gayya daga bangaren Al-Kaida, wanda ya zo sa'o'i kalilan bayan nasarar hallaka mutane biyar da ake kyautata zato masu kishin addinin musulunci ne da sojojin gwamnati suka yi. Tun dai a farkon wannan shekarar ta 2012 ne gwamnatin Yemen ta sa kafar wando guda da masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci inda ta far musu a lardin da taimakon mayakan sa kai na kabilun Abyan, tare da nasarar mayar da lardin karkashin ikonta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala