1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salwantar rayuka lokacin neman tayar da bam a Sokoto

May 23, 2012

Mutane biyu sun mutu a sokoto lokacin wani taho mu gama da 'yan bindiga da suka nemai tayar da abu mai kama da bam. Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhaki ya zuwa yanzu.

Local officials remove the body of a victim from the back of a bus, in front of Aminu Kano teaching hospital in Nigeria's northern city of Kano April 29, 2012. Gunmen killed at least 15 people and wounded many more on Sunday in an attack on a university theatre being used by Christian worshippers in Kano, a northern Nigerian city where hundreds have died in Islamist attacks this year. REUTERS/Stringer(NIGERIA - Tags: CRIME LAW RELIGION TPX IMAGES OF THE DAY)
bama-bamai sun daɗe suna salwantar da rayuka a NajeriyarHoto: REUTERS

A Jihar Sokoton Najeriya, wasu matasa fiye da 10 da ba a tantance ko su wane ba dauke da bindigogi sun kashe mutane biyu a safiyar wannan larabar ciki kuwa har da ɗan sanda, a kusa da Ofishin AIG na 'yan sanda dake kula da jihohin Sokoto kebbi da Zamfara. 'Yan bindigan sun kashe mutanen biyu ne bayan sallar asuba a lokacin da suka yi ƙoƙarin hana su ɗana wani Abu da ke fashewa,da ake kyauta zaton cewa Bomb ne.

Kwamishinan 'yan sandan Sokoto Sanda Aliyu ya bayyana cewar suna ci gaba da bincike don gano ko su waye ke da alhakin aikata aika-aikar. kawo yanzu dai babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin wannan yunƙuri na tayar da abu mai kama da bam. Sai dai Ahmed Aruwa da ke cikin waɗanda suka yi taho mu gama da 'yan bindigan ya bayyana takaicinsa game tabarbarewar tsaro a sokoto.


A daren jiya talata ma dai wasu 'yan fashi da makami suka yi wani fashi a wani Shagon sayar da magani Mai suna Zumunci a tsakkiyar Birnin sokoto, wanda ke zama irin sa na biyu a cikin kwannakki 3 da suka gabata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas