Bakin haure 500 sun kubuta a Libiya
August 1, 2018Talla
Ayoub Qassem da ke magana da yawun sojan ruwan kasar ta Libiya ya bayyana labarin kubutar da mutanen ga kamfanin dillancin labaran Reuters.
Ya ce cikin bakin hauren akwai maza 388 da mata 66 da yara 16. Jiragen ruwa biyu ne aka gansu ba nisa da garin Zawiya da wani jirgin a kusa da Qarabulli. Qassem ya ce bakin hauren sun fito ne daga kasashen Afirka dabam-dabam.
An dai samu raguwar bakin haure da ke barin gabar tekun a Libiya tun daga shekarar 2017 a kokarin da suke yi na gudun talauci da yake-yake da neman ingantacciyar rayuwa a Turai.