1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zargin cin hanci a kudin inganta muhalli a Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB
September 17, 2024

A Najeriya mumunar barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihohi da dama duk da makudan kudi har Naira bilyan 40 da gwamnatin kasar ta bai wa jihohin a cikin shekera guda domin gudanar da aiyukan kare irin wadannan matsaloli.

Najeriya | Ambaliyar ruwa a Maiduguri
Ambaliyar ruwa a Maiduguri da ke NajeriyaHoto: Audu Marte/AFP

Mumunan barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihohin da daman a Najeriyar musamman waccve aka yi a Maiduguri babban birnin jihar Borno ya sanya daga ‘yar yatsa a kan makudan kudadden da gwamnatin Najeriya ta kebe a asusun nan na aiyyuka kare matsalolin da suka shafi muhalli. Domin ofishin kididdiga jama'a na Najeriyar ya bayyana cewa a cikin shekara guda an baiwa jihohi 36 na Najeriyar Naira bilyan 39.62 a matsayin kudadde daga wannan asusu.

Kabin Bayani: Birnin Maiduguri ya fuskanci ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa a Maiduguri da ke NajeriyaHoto: Ahmed Kingimi/REUTERS

Kalo dai ya koma sama a kan gwamnonin jihohin Najeriya da ake baiwa wadannan kudadde daga asusu na musamman na alkinta muhalli. Domin da yawa cikin gwamnonin ana masu kalon kun ci dubu sai ceto in dai magana ce ta kudadden da ya kamata su aiwatar da aiyukan da za su taimakawa alumm'arsu. To sai dai ga Dr Yahya Isaq Maishanu mai taimakawa na musamman ga gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa akwai bukatar fahimtar lamarin.

Abubuwan da suka faru sun zama tamkar fargar jaji ga gwamnatin Najeriya da ke ta kame-kame a kan matakan da ya kamata a ce an dade da dauka sanin bayanai na kimiyya da ke bayyana alamu na afkuwar irin wadannan matsaloli. A kowace shekara dai matsalolin da suka shafi muhalli musamman na ambaliyara ruwa kara muni suke yi a Najeriya musamman mumunar ambaliyar ruwa a jihohin da a shekarun baya-bayan matsalar take masu bakuwa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani