Sama da masu zanga-zanga 50,000 ke taro a Cologne
April 22, 2017Sama da masu zanga-zanga 50,000 ne ake tsammanin su bayyana a birnin Cologne na nan Jamus a wannan rana ta Asabar inda masu adawa da manufofin jam'iyya mai kyamar baki AfD, za su yi gaba-da gaba da magoya bayan jam'iyyar da ke shirin taro mafi girma ga jam'iyyar a tarihinta na shekaru hudu.Kimanin 'yan sanda 4,000 ne dai aka jibge a wannan birni domin kaucewa taho mu gama da ake tsammani tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta AfD mai buri na Turai sai 'ya'yan Turai da masu adawa da wannan manufa ta jam'iyyar.Hannelore Kraft, firemiyar jihar North-Rhine Westphalia, jihar da za a yi taron a cikinta da jagoran jam'iyyar Green Cem Ozdemir ana sa ran za su yi jawabi a taron da zai adawa da manufofin na AfD a wannan rana ta Asabar.Taron na kwanaki biyu dai na zuwa ne bayan da jagorar ta jam'iyyar kin jinin bakin Frauke Petry ta bada sanarwar cewa ba ta niyya ta jan ragamar jam'iyyar a zaben da za a yi na gama gari a watan Satimba a nan Jamus.