Somaliya: Mutane sama da 30 sun halaka
June 20, 2023Talla
Daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu dai, har da wadanda wani rikici da ya barke a jihar Puntland mai kwarya-kwaryan 'yanci ya rutsa da su baya ga wadanda hare-haren bama-bamai da ka kai a yankin Shabelle ya shafa. A Puntland din dai kazamin fadan da ya kaure a Garowe babban birnin jihar, na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan majalisar jihar ke tafka muhawara a kan kundin tsarin gudanar da zabe.