1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140811 Syrien Latakia Angriff

August 16, 2011

Sojojin ƙasar Siriya na ci gaba da cin zarafin masu adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ta hanyar samame da farmaki da suke kaiwa birane daban-daban. Harin garin Latakia a ƙarshen mako ya kashe mutane 26

Hoto: dapd

Duk da kiraye kiraye da ƙasashe da ƙungiyoyin Duniya ke yi wa shugaban Siriya Bashar al-Assad na dakatar da amfani da ƙarfin soji akan masu boren adawa da gwamnati,  Sojojin ƙasar na cigaba da cin zarafin 'yan adawan. Garin Latakia  mai tazarar KM 250 daga birnin Damaskus ta arewaci, nan ya fuskanci somamen Dakarun gwamnatia karshen mako. ayayinda yau aka afkawa gunduwar Homs, a cewar masu kare hakkin jama'a.

Rahotannin da ke fitowa daga Siriyan na nuni da cewar Tankunan Dakarun ƙasar sun afkawa gunduwar Homs, da harbin bindigogi adaidai lokacin da birane daban-daban na Siriyan ke fuskantar gangamin adawa da gwamnatin Bashar al-Assad, yini guda bayan da ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama suka ce an kashe sama da mutane 20 a birnin na Latakia dake arewacin birnin Damascus. Kamar yadda wani mazaunin garin kuma wanda ya ganewa idanunsa ya shaidar.

Hoto: picture alliance/dpa

"Da safiyar yau sojoji da wasu jami'an tsaro sun mamaye wannan gari daga ɓangarori daban-daban.Suna ta buɗe wuta, sun kashe mutane masu yawa tare da raunana wasu. Akwai waɗanda aka karkashe su amma ba zamu iya kwashe gawarwakinsu ba saboda tsananin harbin bindiga".

 Adaidai lokacin da boren 'yan adawan na Siriya ke cika watannin biyar da ɓarkewa , ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama  sun shaidar da cewar 'yan bindiga daɗi sun harbe wani tsohon mutum a garin Hula, a yayinda wasu rahotanni ke bayyana irin kashe-kashen da aka yi a garin na Latakia.

Wata ƙungiyar kare hakkin jama'a dake da matsugunninta a Britaniya ta ce yanzu haka garin na Hula dake gunduwar Homs na cikin mawuyacin hali dangane da somamen Dakarun gwamnatin Siriyan.

A yanzu haka dai mutane na cigaba da tserewa daga  Latakia dake zama cibiyar tashoshin jiragen ruwa na Siriyan, inda wadanda suka gani da idanunsu suka ce sojin da suka ɓalle daga rundunar da gwamnati da kuma masu mubayi'a ga al-Assad ke cigaba da dauki ba dadi tsakaninsu, kamar yadda wannan mutumin ya shaidar.

Hoto: picture alliance / dpa

" Sojojin da suka ɓalle daga na gwamnati suma suna ɗauke da makamansu. Mutane  suna amfani da jiragen ruwa wajen neman mafaka daga wannan bata kashi. A bakin tekun akwai jiragen ruwa wanda ke ɗauke da sojin ɓangarorin biyu. Akalla mutane 60 zuwa 70 a cikin jirgin".

Mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗunkin Duniya, Chris Gunnes ya bayyana cewar, rahotanni daga sansanin 'yan gudun hijira na Ramel, na nuni da mawuyacin hali da mutane ke ciki sakamakon harbe-harben tankokin yaƙi  da ya kewaye sansanin, da kuma daga  cikin jirgin ruwa dake Tekun.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Spain ya ruwaito yadda gwamnatin kasar ta aike da jakada na musamman zuwa wajen Shugaba Bashar al-Assad a watan daaya gabata, domin shawo kansa na amincewa tafiya neman mafaka da Iyalinsa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita           : Umaru Aliyu