1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Diflomasiyya inda ba dimukuradiyya?

Salissou Boukari LMJ
August 19, 2026

Jamhuriyar Nijar da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya PNUDD, sun rattaba hannu kan batun karfafa hulda a kokarin Nijar din na inganta harkokinta na diflomasiyya.

Jamhuriyar Nijar | Janar Abdourahamane Tiani | Raya Kasashe
Shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Hukumar da ke kula da harkokin ci-gaba ta duniya ta amince da tallafa wa wannan cibiya, domin Jamhuriyar ta Nijar ta ci moriyarta a fannin kwarewa kan harkokin diflomasiyya da hulda tsakanin kasa da kasa.

Cibiyar diflomasiyya a inda babu dimukuradiyya?

Tun dai a ranar 23 ga watan Janairun 2026 ne, Nijar ta buda Cibiyar Horas da Jami'an Diflomasiyya a fannoni dabam-dabam da nufin kasar ta samu cikakar mafita har ta yi zarra a fannin harkokin diflomasiyya a tsakanin kasashe. Ana dai ganin rattaba hannu na amincewa juna tare da hukumar da ke kula da harkokin ci-gaba ta Majalisar Dinkin Duniyar, a matsayin wata babbar dama ga Nijar.

Maradi: Lalacewar titi na shafar sufuri

02:53

This browser does not support the video element.

Ministan harkokin kasashen waje na Nijar din Bakary Yaou Sangare ya ce, karfafa harkokin diflomasiyyar kasarsa na daga cikin sabon tsarin da suka sa a gaba a fannin harkokin ci-gaba. A cewarsa, in har za a kare muradun kasar da isar da muryoyin al'ummarta zuwa sauran kasashen duniya, dole sai an samar da jami'ai da suka samu sani da kwarewa a wannan fanni.

Amincewar 'yan adawa

Masu adawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar kamar kungiyar nan ta G25 da Tahirou Garka ke magana da yawunta, na ganin duk kasa mai son ci-gaba dole ne sai ta san hanyoyi na karfafa diflomasiyya da nufin kauce wa manyan kura-kurai da ke mayar da kasa baya. Ita dai wannan Cibiya ta Horas da Jami'an Diflomasiyya ta  Nijar da har yanzu ake kokarin kafa ta, an samar da ita ne ta hanyar hulda da kasar Maroko da ita ma ke da sanannar cibiyar da ta kware a fannin koyar da aikin diflomasiyya.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW