1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki na samar da lantarkin Najeriya

Uwais Abubakar IsrisNovember 3, 2015

Akwai wani sauyi da aka samu tun bayan mayar da bangaren samar da wutar lantarkin Najeriya zuwa ga 'yan kasuwa.

Nigeria Strom Elektrizität Energie Generator Lagos
Hoto: picture-alliance/dpa

Shekaru biyu ke nan da gwamnatin Najeriya ta sayar da sashin samar da wutar lantarkin inda ta mika shi a hannun kamfanonin ‘yan kasuwa tare da alkawarin samun ingancin wutan lantarki a kasar. Shin ya tafiyar ta kasance a yanzu ko an fara samun sauyi?

Mayar da wannan sashi a hannun ‘yan kasuwa da gwamnatin Najeriya ta yi shekaru biyu da suka gabata ya sanya rarraba wannan sashi zuwa kamfanonin 18, guda 11 daga ciki suna aikin rarraba wutar, shida suna samar wa yayin da gwamnatin ta rike guda daya da ke dakon wutar.

Tun da wannan lokaci an fuskanci kwan-gaba kwan-baya a harkar yawan wutar da Najeriya ke samar duk da cewa ta karu har zuwa sama da megawatt dubu biyar daga dubu biyu da a baya ake samu. Wani ci-gaba aka samu cikin wannan lokaci? Malam Ahmed Ibrahim Shekarau shi ne jamai'in hulda da jama'a na kamfanin rarraba wuta lantarki na yankin Abuja:

"An samu ci-gaba sosai domin shigowar wannan gwamnati masu fasa bututun wata-kila saboda gwamnatin da shugaban da suke gani matsalar ta yi sauki sosai. A yanzu muna kai har megatawatt dubu biyar da wani abu, muna sa ran zama mu iya kawai dubu shida"

To sai dai fa ‘yan Najeriya da dama na masu ra'ayin cewa akwai sauran aiki abin da ya sanya na leka kasuwar Wuse da ke Abuja inda na iske injinan janaraito na kara saboda dauke wutar.

Hoto: picture-alliance/dpa

A gefe guda Malam Shehu Tela Zaria wanda dauke wutar ya sanya shi dage kafarsa daga sana'arsa inda ya ce a farkon wannan gwamnati an fara samun ingantuwar lamura.

Kwarararru a fanin samar da wutar na masu bayyana cewa babban kalubale da ke fuskantar wannan sashi shi ne na rashin ingancin hanyoyin rarraba wutar.

Najeriya tana da sauran aiki a fanin samar da wutar duk da mayar da harkar hannun ‘yan kasuwa, domin kasar na samar da abin da bai kai megawatt dubu shida ba ga al'umma milyan 170 in aka kwatanta da Afrika ta kudu mai samar da megawatt na wuta dubu 50 ga al'ummarta mai yawan milyan 40, abin da ya sanya kwarraru bayyana bukatar rungumar tsarin samar da wutar lantarki ta hanyar da ake sabuntawa.