Mafita kan rikici da Fulani a Najeriya
May 10, 2019
Wannan dai na zuwa ne a wani mataki na gujewa harin ramukon gayya biyo bayan kashe daruruwan shanun Fulani a wasu yankunan jihar Filato da ma wasu jihohin arewa maso tsakiya.
A wani taron manema labarai a birnin Jos, jim kadan bayan sun kammala tattaunawa kan matakan dalike ci gaban hare-haren, shugabannin kungiyar makiyayan sun bayyana cewar duk da cewar makiyaya ake wa hassarar rayuka da dabbobia kullum, to amma za su tabbatar da samun zaman lafiya, maimakon ramukon gayya.
Kasancewar shugabanin makiyayan sun ci alwashin isar da wannan sako na zaman lafiya ga sauran Fulani da ke rugage. A makon da ya gabata ne dai a jihar Filato makiyayan suka yi korafin kashe musu daruruwan shanu tsakanin yankunan Jos ta Kudu da Bassa, inda kuma hukumomin tsaro tare da gwamnatin Filato suka yi kokari wajen shawo kan lamarin.
Shugabannin kungiyar makiyayan sun ci alwashi cewar tare da matakai da suke dauka a yanzu za a sami saukin tashe-tashen hankula a wannan yankin, mussaman wajen magance rikicin manoma da makiyaya da ka iya tasowa, ganin yadda damina ke karatowa.