1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaddamar da sabon taken Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa SB/AMA
June 22, 2023

Majalisar dokokin ta kaddamar da sabon taken kasa wanda kasar ta samar domin maye gurbin wanda kasar ta gado daga Turawan mulkin mallaka na Faransa.

Jamhuriyar Nijar I Yamai | Majalisar Dokokin
Majalisar Dokokin Jamhuriyar NijarHoto: Gazali A. Tassawa/DW

A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta kaddamar da sabon taken kasar wanda kasar ta samar domin maye gurbin wanda ta gada daga Faransa. Illahirin 'yan majalisar dokokin kasar na bangaren masu mulki da adawa suka kada kuri'ar amincewa da sabon taken bayan yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Karin Bayani: Nijar: Mika sabon taken kasa ga majalisa

Sabon taken Jamhuriyar Nijar mai suna "l'Honneur de la Patrie" wanda gwamnatin kasar ta shigar da shi a gaban majalisar dokokin kasar domin samun amincewarta. Da kuri'u 149 ne majalisar dokokin ta kada kuri'ar amincewa da sabon taken wanda ke rubuce a saman shedara 21 da kuma a karanci ke daukar tsawon minti daya da sakonni 41. Assoumana Malam Issa tsohon ministan raya al'adu kana memba a kwamitin rubuta sabon taken kasar ta Jamhuriyar Nijar, ya bayyana wasu daga cikin sakonni da sabon taken ke isarwa.

Duk da yake cewa 'yan majalisar dokokin adawa sun kada kuri'ar amincewa da sabon taken kasar ta Jamhuriyar Nijar, Honnorable Soumana Sanda na jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka, ya gargadi gwamnati kan cewa sauya take ba wani sauyin da zai haifar ga kasar matsawar gwamnatin ba ta sauya hali ba. 'Yan kasa da dama ne dai suka hallara a zauran majalisar dokokin domin halartar mahawara da kuma kaddamar da sabon taken kasar.

Bayan kaddamar da sabon taken a gaban majalisar dokoki, ba za a soma aiki da shi ba a bainal jama'a sai bayan shugaban kasa ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta haifar da sabon taken nan da makonni biyu masu zuwa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani