1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da sulhu a Yankin Gabas ta Tsakiya

May 23, 2011

Ƙasashen Turai sun ce guguwar sauyin da ke kaɗawa a ƙasashen Larabawa wata dama ce na tabbatar da sulhu da zaman lafiya a yankin

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yana hira da manema labaraiHoto: dapd

Ƙungiyar Tarayyar Turai, a yayin da take maraba da manufofin Amurka dangane da Yankin Gabas ta Tsakiya wanda shugaba Obama ya gabatar a jawabin sa dangane da yankin, ta yi kira ga ƙungiyar manyan ƙasashen duniya da su gudanar da taron gaggawa wadda zata samar da yarjejeniyar sulhu tsakanin Israila da Falasɗinu.

A wata sanarwar da ministocin kula da harkokin wajen ƙasashenTurai guda 27 suka wallafa, sun ce jawabin shugaba Obama ya fayyace batutuwan da suka fi mahimmancin wajen tafiyar da tattaunawar, kuma sun bayyana amincewar su da sulhun da aka samu a baya-bayan nan tsakanin shugabanin Falasɗinu na Fatah da Hamas. Hakanan kuma ƙasashen sun ce rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasashen larabawa yanzu sun nuna mahimmancin gaggauta samar da sulhu a yankin, kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bayyana

 "Wannan wata taga ce ta dama da aka samu, wadda ka iya rufe kanta a cikin lokaci kaɗan. Wannan sauyi da ake samu a ƙasashen larabawa ya bada damar cigaba da tattaunawar sulhu a Yankin na Gabas Ta Tsakiya. Saboda haka wajibi ne a yi amfani da wannan damar domin tabbatar da nasarar guguwar neman sauyin da ke kaɗawa".

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita:            Umaru Aliyu