1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arbeitstitel: Abschlussbericht Gipfelkonferenz zur Nuklearen Sicherheit

March 27, 2012

Manyan kasashen duniya na nuna fargabar fadawar makaman nukiliya hannun 'yan ta'adda saboda barazanar da yake da shi ga rayuwar al'ummomin kasa da kasa

U.S. President Barack Obama speaks during a joint news conference with South Korea's President Lee Myung-bak at the Blue House in Seoul March 25, 2012. Obama arrived in Seoul on Sunday to attend the Nuclear Security Summit, a follow-up to the summit he held in Washington in 2010. REUTERS/Yuriko Nakao (SOUTH KOREA - Tags: POLITICS MILITARY)
Shugaba Barack ObamaHoto: Reuters

Shugaba Obama na Amurka ya yi kira ga kasashen duniya su karfafa hadin kai a bangaren kare duk wata barazana ta harin ta'addanci na nukiliya. Wannan kiran na Shugaba Obama ya zo ne yayin rufe taron kolin da aka bude game da tsaron nukiliyar a Korea ta Kudu.

Shugaba Obama ya ce wannan kiran ya zama dole ganin cewar 'yan ta'adda na iya amafani da makaman nukiliya wajen hallaka bayin Allah da ba su ji ba su gani ba, a saboda haka ya ce dole ne shugabanin kasashen duniya su tashi tsaye wajen ganin magance wannan lamari ta hanyar daina amfani da sinadarin Uranium da za iya yin makamin nukilya nan da shekaru hudu masu zuwa.

"Shugaba Obama kenan inda ya ke cewa kowa zai amince cewar har yanzu barazanar na nan, har kawo wannan lokacin akwai batagari da su ke neman sinadaran hada makaman nukilyar ruwa a jallo kuma wadannan makamai na da mautukar hatsari a wurare da dama".

Baya ga wannan damuwa da shugaban ya nuna game da shigar makaman nukilya hannun 'yan ta'adda, ya yin taron shugabannin sun amince da a rage amfani da sinadarin uranium musamman ma dai wanda za a iya amfani da shi wajen yin makamin kare dangi. Sakamakon wannan yarjejeniya da aka cimma ne ma Amurka ta amince za dinga samawa Faransa da Belgium sinadarin uranium wanda ba za iya amfani da shi wajen kera makamai ba don kasashen biyu su yi amfani da shi wajen binciken da ya danganci fannin lafiya.

Hoto: Reuters

Dorewar matakin da shugabanin kasa da kasa suka dauka

To sai dai duk da cewar shugabannin sun cimma matsaya kan wannan batu, a gefe guda masu sharhi na ganin cewar daukan matakin da aka yi tamkar yin tuya ne ba a sa albasa domin a cewarsu kawo wannan lokacin babu wata doka da aka fitar a duniya da za yi amfani da ita hana bazuwar sinadarin.

To duk da cewar akwai wannan kalubale, Shugaba Obama ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen cimma nasarar da su ka sanya a gaba wajen kare Amurka da kawayenta da ma sauran kasashen duniya daga wannan barazana.

"Ya ce za mu tabbatar da tsaron Amurka da kawayenta da ma sauran kasashe da kuma yunkurin kare kawunan mu daga duk wata barazana sannan za mu dukufa wajen ganin mu rage yawan makaman nukiya".

Ita ma dai Burtaniya ta yi bi sawun Amurka wajen ganin sinadaran ba su bazu ba musamman ma a hannun 'yan ta'adda, ta ku ce za ta bada wannan gudummawa ce wajen taimakawa kasashen duniya da dabarun da ta ke da su na fasakaurin sinadaran da ake hada makaman kare dangi. Mataimakin Prime Ministan na Burtaniya Nick Clegg ne ya ambata hakan wajen bikin rufe taron, abin da shugabannin duniya da dama su ka yi maraba da shi cike da fatan hakan zai taimaka wajen samun nasarar da aka saya a gaba.

Shirin Koriya ta Arewa na harba tauraron Dan Adam

Yayin da kasashen duniya ke kokarin ganin sun cimma wannan buri, a gefe guda Koriya ta Arewa ta lashi takobin harba tauraron dan adam, abin da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da Koriya ta Kudu su ka bayyana da cewar wata dabara ce kawai ta gwajin harba makamin nukilya, inda su ka yi Allah wadai da shi tare da bayyana cewar wannan mataki da za su dauka ya saba da kudurorin da aka cimma a zauren Majalisar Dinkin Duniya game da haka.

Sai dai duk da wannan, mahukunta na Pyongyang sun dage a kan cewar tauraron dan adam za su harba a wani mataki na bikin cika shekar dari da haihuwar wanda ya kafa Kim Sung na Biyu wanda ke tafe cikin wata mai kamawa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi