1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci tabbacin tsaro a Sudan

Zainab Mohammed Abubakar
May 3, 2023

MDD ta nemi tabbacin tsaro don isar da kayan agaji da ake bukata a Sudan mai fama da rikici, bayan wawashe manyan motocin kayan abinci zuwa yankin Darfur.

Jordanien Amman | ICRC-Mitglieder bereiten humanitäre Hilfsgüter für den Sudan vor
Hoto: ICRC/AFP

Babban jami'in jinkai na MDD Martin Griffiths ya jaddada bukatar hakan, don tabbatar da cewar kayan agajin sun isa ga jama'a mabukata, a karkashin kariyar sojoji a wani mataki na kare tsarin jinkai don isarwa inda suka dace.

Duk da cewar bangarorin da ke fada da juna sun amince da sabon shirin tsagaita bude wuta na kwanaki bakwai daga gobe alhamis, tun a safiyar wannan Larabar an ji karar hare-haren ta sama a birnin Khartoum, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya shaidar, wanda ke dasa ayar tambaya game da yiwuwar daraja yarjejeniyar.

Ya zuwa yanzu dai wannan rikici ya haifar da matsalar bukatar jinkai na gaggawa, tare da tilasta  wa mutane 100,000 tserewa zuwa kasashe da ke makwabtaka ba tare da isasshen abinci ko ruwa ba, inji Majalisar Dinkin Duniya.