1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sammacin cafke jami'an Libiya

June 27, 2011

Kotun ICC ta bayar da umarnin cafke shugaba Gadhafi na Libiya

Luis Moreno Ocampo,babban mai shigar da ƙara na kotun ICCHoto: dapd

Kotun sauraron manyan laifuka ta duniya ko kuma ICC wadda ke da mazauni a birnin The Hague na ƙasar Holand ta bayar da sammacin cafke shugaban ƙasar Libiya Mouamer Gadhafi, tare da babban ɗansa Saif al-Islam da kuma shughaban hukumar leƙen asirin ƙasar bisa zargin su da laifin aikata manyan laifuka akan bani Adama. Wannan dai shi ne karon farko da kotun ke bayar da sammacin daya danganci rugingimun dake ci gaba da afkuwa a ƙasar ta Libiya.

Tun a watan jiya ne babban mai shigar da ƙara a kotun Luis Moreno - Ocampo ya buƙaci kotun ta bayar da umarnin cafke manyan jami'an bayan wani binciken da ta gudanar, wanda ya nuna cewar an aikata kissar gillar masu boren nuna adawa da gwamnati - da gan-gan. Wannan sammacin ya zo ne a dai dai lokacin da aka cika kwanaki 100 tun bayan da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta ƙaddamar da hare-hare akan Libiya, wanda ta ce ke da nufin kare fararen hular ƙasar ne.

A halin da ake ciki kuma, wasu rahotanni na cewar an sami sabbin hare-hare a tsakanin dakarun dake biyayya ga shugaban na Libiya da kuma 'yan tawayen ƙasar a yankin kudu-maso-yammacin birnin Tripoli. Kwamandojin 'yan tawayen suka ce bata-kashin na mayar da hankali ne akan garin Bir al-Ghanam, wanda ke zama muhimmin wuri a kan hanyar zuwa birnin Tripoli, fadar gwamnatin ƙasar ta Libiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala