EU: Samar da hanyar raba bakin haure
September 23, 2019![Malta EU-Treffen der Innenminister | Horst Seehofer, Deutschland](https://static.dw.com/image/50549260_800.webp)
Talla
Ministan harkokin cikin gida na Maltan Michael Farrugia ne ya bayyana hakan, inda ya ce shi da takwaransa na Jamus Horst Seehofer sun amince da yarjejeniyar da za a gabatar domin tattaunawa yayin taron ministocin cikin gida na kasashen kungiyar EU a ranar takwas ga watan Oktoba mai zuwa. Sai dai ya ce amincewar tasu ba za ta yi amfani ba, matukar ba a fadada abin domin amincewar sauran kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar turai EU ba. Shi ma a nasa bangaren ministan cikin gida na Jamus din Horst Seehofer ya sanar da cewa tsarin zai kasance na watannin shida, kuma za a kaddamar da shi da zarar sauran kasashen kungiyar ta EU sun amince.