Kamaru ta yi sabon jagoran kwallon kafa
December 13, 2021Tsohon tauraron kungiyar Barcelona ta Spain kuma tsohon zakaran kwallon kafa na Afirka, A wasan tseren motoci na Formula 1 da ya gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa kuwa, Max Verstappen ya samu nasarar samun kambun. Wanda ya samu nasarar a wasan da ya wakana a birnin Abu Dhabi zai mamaye komai, abin da ya saka Max Verstappen ya samu nasara kan Lewis Hamilton. Samuel Eto'o Fils ya samu nasarar zama shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kamarun ne, yayin zaben da aka gudanar a ranar Lahadin karshen mako. Ita kuwa Guinea ta nada Kaba Diawara ne a matsayin mai horas da 'yan wasan kwallon kafar kasar, wanda shi ma ya kasance tsohon shahararren dan wasa. A hannu guda kuma, Hukumar Kula da KWallon Kafa ta Najeriya ta sallami mai horas da 'yan wasan kasar Gernot Rohr dan kasar Jamus. Korar tasa dai nai zuwa ne, yayin da ake shirin fara wasan neman cin kofin kwallon kafa nahiyar Afirka.
A wasannin lig na Bundesliga da aka kara a Jamus kuwa, Bochum da Dortmund sun tashi kunnen doki daya da daya kana Wolfsburg ta yi rashin sa'a a gida, inda Stuttgart ta doke ta da ci biyu da nema. A nata bangaren kungiyar Bayern Munich ta doke Mainz da ci biyu da daya, sannan Leipzig ta yi raga-raga da Monchengladbach da ci hudu da daya. Tsohon kwamishinan kula da shri'a na kungiyar Tarayyar Turai, Franco Frattini ya ce hada karfi kawai zai kawo karshen cin-hanci a bangaren wasanni. Dan kasar Italiya wanda yanzu yake kungiyar tabbatar da tsari a bangaren wasanni na duniya, yana gani idan aka yi sa a cin-hanci zai dagula harkokin wasanni a duniya.