Sana'ar dinki don dogaro da kai
February 10, 2016 Matasa sun kasance kashin bayan ko wace alumma, matasan Nigeria a yanzu sun farka daga barci ta neman dogaro da kai maimakon zaman kashe wando ko kuma tumasanci a tsakanin al'umma Ibrahim Abubakar mai dinki ne kuma yana zaune ne a anguwar Obalende. Ibrahim dai mai shekaru 38 a duniya ya kasance mai hangen nesa tare da daukar mataki na zama mutum mai cike da alfahari na dogaro da kai abun misali .Yana da katafaren shagon dinki a yankin Obalende tare da kawunan dinki a kalla shida, inda matasa ke cigaba da gudanar da aikin su batare da kakkautawa ba .
Babu shakka sannaar hannu ita ce abun dogaro ga misalai da masana ilmi ke faman bayyana wa, ga duk taro da ake neman magance rashin aikin yi ga matasa. Alhaji Ibrahim dai ya yi wa DW karin bayani a dangane da gudummowa da yake bayarwa a anguwar da yake da zama.
"Yace gudumawa ta ga yankin da na fito ta kasance ta fannin koyar da matasa sanaar dinki da kuma tallafi ga al'umma idan har hakan ta taso"
Bugu da kari Ibrahim ya bayyana kukansa ga gwamnatin Nigeria, musamman ta samar da kafa da za ta bada tallafi ga matasa domin shiga sana'ar hannu, ta inda za su rage zama karkashin bishiya ko maula ga masu akwai a cikin kasa.
Bayan lura da yadda matasan ke baje basirarsu a cikin shagon dinki na tsinkayi daya daga cikin matasan da ke aiki a shagon mai suna Muhammad. Inda yace a cikin wannan sana'a yana samun kwanciyar hankali tare da abun rufa asiri musamman ta hanyar neman abinci da kuma biyan kudin makaranta ga yara kanana. Bincike dai ya nunar da cewa sana'ar hannu babu ko shakka, ta zarta aiki irin na gwamnati ko kamfani domin babu batu na ritaya komai tsufa.