1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kebbi: Matashi mai kera tuka-tuka

June 26, 2019

Wani matashi daga jihar Kebbi da ya kammala karatunsa na jami'a ya jingine kwalin digirinsa ya kuma rungumi sana'ar kera tuka-tuka na gargajiya ga mutanen yankinsu a wani mataki na saukaka masu wahalhalun samun ruwa.

Zimbabwe Afrika Armut
Injin tuka.tuka domin samar da ruwan shaHoto: AP

Matashin dai Muhammadu Kabiru da ya kammala karatunsa a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce  yanzu haka kusan shekaru tara kenan ya shafe yana gudanar da wannan sana'a ta kera tuka-tukan na gargajiya a kauyensu  mai suna Natsini Gada da ke da nisan kilomitoci kalilan daga garin Argungu a jihar Kebbi, lamarin da yasa matsalar ruwa ta kau ga baki dayan kauyen  nasu.
                                                
Yanzu haka dai wannan matashi ya saukakawa al'umma da dama dangane da magance masu matsalar ruwa a kauyen nasu da ma sauran makwabata. Koda yake matashin ya ce aikin samar da wannan tuka-tukan na gargajiya ba abu ne mai sauki ba, domin ko yana tattare da kalubale irin nashi.
                                                            
Ba yagama dinbim matasan da ya horar ga wannan sana'a, suma al'ummar gari na cin gajiyar baiwar tasa. DW ta yi nasarar tattaunawa da kadan daga cikin masu gidajen da ke anfanuwa da wannan tuka-tuka na gargajiya. Al'ummar garin na Natsini Gada dai na ci gaba da yabawa wannan matashin kan yadda wannan fasaha tashi ta daukaka wannan gari nasu a idon al'umma.