1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Bukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara

December 21, 2023

Kwanaki kalinan gabanin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, matan aure masu sana'ar kwalliyar fuska da kitso da gyaran gashi na cin kasuwa a irin wannan lokaci.

Najeriya | Kaduna | Kirsimeti | Sabuwar Shekara
Kkayan ado da kawata gidaje da wurare yayin bukukuwan KirsimetiHoto: DW/G. Hilse

Duk da yanayin karancin kudi da tsadar rayuwa dai, matan da suka rungumi wadannan sana'o'i na samun abun rufawa kansu asiri tare da taimakon mazajensu wajen yiwa yara kayan shagul-gulan bukukuwan Kirsimetin da sabuwar shekara domin karfafa soyayaya. Madam Blessing Toyin na da wani katafaren shagon kwalliyar fuska a kasuwar Barnawa Kaduna, ta nunar da cewa tana samun tururuwar mata a shagonta domin gyara fatar jikinsu. Ta ce ta wannan hanyar suke samun kudin ciyar da kai tare da daukar dawainiyar kulawa da sauran 'ya'yansu.

Wannan kasuwa ta kirsimeti na bai wa mata masu kananan sana'o'in hannu damar samun kudin daukar dawainiyar kulawa da 'ya'yansu da mazajensu, domin rage fatara da talauci tare da magance matsalar zaman rashin aikin yi. Madam Mary James Okoro matar aure ce da ke da wani katon shagon kitso da wanke kai na mata irin na zamani a Kadunan Najeriya, ta ce wannan lokacin na taimaka musu wajen samun abin rufawa kai asiri. Ta kuma karfafawa mata gwiwar rungumar kananan sana'o'in dogaro da kai. Yayin da 'yan mata ke zuwa wuraren yin kwalliya da gyaran fatar jiki a irin wannan lokacin na kokawa da tsadar kayayyaki sakamakon hauhawar farashin kudin kasashen ketare da ke shafar harkokin kasuwancin Najeriya, a bangare guda samari na tserewa 'yan matan ne a irin wannan lokacin saboda tsadar rayuwar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani