1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanders ya yi watsi da burin yi wa Democrat takara

Mohammad Nasiru Awal AS
April 8, 2020

Bernie Sanders ya yi watsi da aniyarsa ta tsaya wa jam'iyyarsa ta Democrat takara a zaben kasar Amirka na karshen shekara.

USA | Wahlen | Bernie Sanders
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Daya daga cikin jiga-jigan neman takarar shugabancin Amirka, Sanata Bernie Sander dan ra'ayin gurguzu ya fice daga takarar neman tsaya wa jam'iyyarsa ta Democrat takarar a zaben shugaban kasar Amirka da zai gudana a karshen wannan shekara.

Wani sako da Sanata Sanders ya wallafa a Twitter na cewa: " A yau na dakatar da yakin neman zabe, amma yayin da kamfen din ya kawo karshe, ana ci gaba da gwagwarmayar neman adalci."

Hakan dai zai ba wa Joe Biden damar tsaya wa Democrat din takara don kalubalantar Shugaba Donald Trump a zaben na watan Nuwamba mai zuwa. 

Wannan mataki da Sanders ya dauka na zuwa ne daidai lokacin Biden ke kara yi masa fintinkau a zabukan tsayar da dan takara, duk da cewa zabukan sun shiga wani hali sakamakon cutar Corona.