1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkakiya da ke tattare da rikicin Sudan

May 5, 2023

Duk da jerin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Sudan, har yanzu haka ta gaza cimma ruwa wajen kawo karshen kazamin fada da ake gwabzawa a kasar.

Sudan Flüchtlingswelle
Hoto: Gueipeur Denis Sassou/AFP

Masu sharhi na ci gaba da martani kan fadan neman iko da ake ci gaba da gabzawa a kasar tsakanin manyan dakarun soji a kasar wato Abdel Fattah al-Burhan da kuma Mohammed Hamdan Dagalo wato Hemedti da ke jagorantar dakarun RSF. Da dama na ganin fadan ba zai kawo karshe ba har sai bangare daya ya samu nasara a kan dayan bangaren.

Ana dai ganin dara ce ta ci gida, inda shekarar 2019 bangarorin biyu da a yanzu ba sa ga maciji da juna suka hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir wanda a wancan lokacin sauka samu goyon bayan jama'a kamar yadda kasashen yammacin Turai ke ganin Sudan din ta dauki hanyar tabbatar da dimokradiyya a kasar.

Sai dai an fidda tsamanin hakan bayan da shugaban rundunar sojin kasar Abdel fattah al-Burhan ya rusa gwamnatin rikon kwarya a shekarar 2021. Sai dai a yanzu da Sudan din ke ci gaba da fadawa cikin rikici, ana ganin akwai hatsarin da makwaftanta ka iya fuskanta, kamar yadda tsohon Firanministan Abdallah Hamdok ya yi ikrari cewa, wannan fada ne tsakanin dakarun da suke da horo da kuma wadanda ke da makamai.

Birnin KhartumHoto: AFP/Getty Images

Ana dai ganin Hemedti na da magoya baya a kasar Sudan domin haka ne wani Kwararre a kasar ta Sudan Aly Verjee ya yi gargadin cewa wuce gona da iri na al'ummar Rizeigat da ke kan iyakar Sudan da Chadi.

Ya ce "Abu ne mai sauki a ce al'umma Rizeigat na da tunani iri daya, shi ya sa zaka ga mutane da zarar cewa wani ya fito daga wannan bangare to tabbas zai goya masa baya. Ba abu bane mai sauki, akwai fargaba tsakanin wadannan kungiyoyin, amma abu mafi mahimmanci shi ne Hemedti na samun ci gaba saboda wasu ba su da karfin fadada da kuma dauka dakarunsa a fadin kasar"

Rundunar RSF na da dakaru kimanin dubu 100 wadanda ke biyaya ga Hemedti kuma suke da sasanoni a sassa daban-daban na kasar. Ana kuma ganin Hemedti na da kyayawar alaka da kasar Yemen saboda yadda ya tura dubban dakaru zuwa kasar domin yakar 'yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran, ko baya ga kasashen Saudiya da kuma hadaddiyar Daular Larabawa da ma kamfanin sojin hayan Rasha na Wagner.

A yanzu haka dai lamura na kara runtsabewa a kan iyakar Sudan, sai dai ana ganin da kamar wuya kasashe irinsu Sudan ta Kudu da Libiya da chadi da kuma Habasha su shiga cikin fadan kasancewar a baya sun fuskanci makamacin wannan rikicin. Sai dai ga Hassan Khannenje, masani a cibiyar nazarin rikice-rikice a yankin kahon Afirka, ya na ganin wasu kasashen ka iya taka rawa wajen sassanta rikicin.

Ya ce " Ko shakka babu, kasar Habasha ba zata shiga rikicin Sudan ba, sai dai idan aka gaza yiwa tufka hanci, za ta kasancewa mai shiga tsakani a kan teburin tattaunawa kuma ta bada gudunmawa, sai dai a wannan lokacin kai tsaye ba zamu ce tana bada goyon baya ba."

'Yan gudun hijirar Sudan da ke bakin ruwaHoto: El Tayeb Siddig/REUTERS

To sai dai Khanneje ya na da yakinin cewa, kasar ta Habasha ka iya nuna goyon bayanta ga gwamnatin farar hula a nan gaba.

Ya kara da cewa "Har sai kasar Sudan ta koma kan tafarkin mulkin farar hula sannan Habasha za ta nuna sha'awar nuna goyon baya wanda hakan za a iya fahimta saboda fargaba kan yankin nan na Al-Fashaga."

Rundunar sojin Sudan dai na da kimanin dakaru dubu 120 da ke da alaka mai karfi da kasar Masar. Masana dai na ganin kasashen da ke bai wa dukannin bangarorin goyon baya na da aiki ja a gabansu da sanya wa bangarorin su amince da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta, inda suka nuna fargabar cewa idan hakan bai yiwu ba cikin makwanni biyu zuwa uku, masu goyon bayan bangarorin da ke fada na kasashen waje za su fara basu tallafin kudi da kuma makamai.