1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkakiyar tallafin ceto ga tattalin arzikin Spain

June 12, 2012

Masu zuba jari a Spain sun baiyana damuwa akan tasirin da jadawalin tallafin ceto da kasashen euro suka baiwa Spain zai yi ga makomar kasar.

epa03257675 Spanish Prime Minister Mariano Rajoy, prior to a press conference held at La Moncloa Palace in Madrid, Spain, 10 June 2012. Asking eurozone partners to bailout Spain's stricken banks was a 'hard, difficult and complicated' decision but "indispensable" to nurse the economy back to health, Prime Minister Mariano Rajoy said 10 June. In a press conference a day after the Eurogroup panel of eurozone finance ministers said up to 100 billion euros (125 billion dollars) would be made available for Spain. EPA/JAVIER LIZON
Firaministan Spain Mariano RajoyHoto: picture-alliance/dpa

Masu zuba hannun jari sun nuna damuwa tare da baiyana cewa murnarsu ta koma ciki a dangane da bashin tallafin ceto da kasashe masu amfani da kudin euro suka baiwa kasar Spain. Masu zuba jarin sun baiyana fargaba akan tasirin da tallafin ceton zai haifar yayin da a ranar Litinin da ta wuce babbar kasuwar hannayen jarin Spain din  IBEX ta dan ja baya. Jadawalin yarjejeniyar dai ya nuna cewa wajibi ne a yiwa dukkanin bankunan Spain din gagarumin garanbawul yayin da hukumomi da cibiyoyi masu rauni za'a rufe su. Hakannan kuma kungiyar Tarayyar Turai za ta sanya idanu sosai wajen tafiyarwar harkokin cibiyoyin kudade a kasar. Manazarta tattalin arziki sun ce tallafin ceton mataki ne na wucin gadi. Masu zuba jarin na nuna damuwa a kan tsawon lokacin da matsalar kudaden zai dauka. A hannu guda kuma ana hangen cewa tallafin ba zai baiwa bankunan kasar ta Spain sukunin neman rance a kasuwannin hanayen jari ba. A maimakon haka zai kara yawan bashi ne akan kasar wanda ke nufin cewa karbar wani tallafi a nan gaba zai kasance mai tsada ga kasar ta Spain.

Mawallafi:; Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi