1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Charles III ya yi jawabi ga majalisar

Binta Aliyu Zurmi
September 12, 2022

A ziyararsa ta farko ga majalisar dokokin Birtaniya a yau, Sarki Charles III ya yi wa 'yan majalisar godiya bisa ta'aziyyar mahaifiyarsa sarauniya Elizabeth II.

England London | Westminster Hall | King Charles III.
Hoto: Henry Nicholls/WPA/Getty Images

Da yake jawabi yayin ziyarar mai cike da tarihi, sarkin ya sha alwashin ci gaba da mutunta majalisar da ma al'adun masarautarsu kamar yadda mahaifiyarsa ta yi bil hakki da gaskiya a lokacin da ta ke raye.

Jin kadan bayan kammala jawabinsa da ma karba ta'aziyar a zauren taro na Westminster, Sarki Charles da mai dakinsa sun kama hanyar Edinburgh da ke yankin Scotland inda akwatin gawar Sarauniya ya ke wanda za a kai majami'ar St. Giles domin al'umma su sami damar yin bankwana da ita.

A ranar Litinin din da ke tafe ne za a binne Sarauniya Elizabeth II a kusa da mijinta wanda ya rasu a shekarar da ta gabata a makabartar da ke Fadar Windsor.