1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
ImaniTurai

Sarki Charles III zai karbi bakuncin Shugaba Tinubu

March 18, 2026

Sarki Charles III na Burtaniya zai karbi bakuncin Shugaban Nigeria, Bola Ahmed Tinubu, a fadar Windsor, a wata ziyara irin ta ta farko ga shugabannin Najeriya cikin shekaru 37, wadda ke da nufin karfafa alakar kasashen

Sarki Charles III na Burtaniya
Sarki Charles III na BurtaniyaHoto: Chris Jackson/Pool via REUTERS

Yayin da kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya kai wani sabon mataki, ana sa ran Sarkin zai jaddada dangantakar al'adu da kasuwanci mai zurfi a lokacin ziyarar kwanaki biyu da Bola Ahmed Tinubu ke yi.

Shugaba Tinubu tare da mai dakinsa Oluremi Tinubu za su samu tarba daga Yarima William da mai dakinsa Gimbiya Catherine ta Wales domin rakiyar su zuwa fadar Windsor.

Gwamnatin Birtaniya na fatan wannan ziyara za ta kara karfafa matsayin ƙasar a matsayin cibiyar kasuwanci ta duniya ga harkokin Afirka.