1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sarki Charles ya jinjinawa al'ummar Ukraine a kan Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 24, 2024

Tuni dai manyan shugagbannin kasashen duniya suka isa birnin Kiev don taya Ukraine jimamin halin da ta samu kanta a ciki

Hoto: Aaron Chown/Getty Images

Sarki Charles na III na Burtaniya ya jinjinawa al'ummar kasar Ukraine bisa juriyar da suke nunawa a daidai wannan lokaci da kasarsu ke cika shekaru biyu da fuskantar mamaya daga sojojin Rasha.

Karin bayani:Duniya na fatan alkahiri ga Sarki Charles

Sarki Charles ya jaddada cewa hakika sun cancanci yabo a cikin wannan mummunan yanayi na ba gaira ba dalilin afka musu.

Karin bayani:An nada Sarkin Ingila bayan shekaru 70

Tuni dai manyan shugabannin kasashen duniya suka isa birnin Kiev don taya Ukraine jimamin halin da ta samu kanta a ciki. Wadanda suka hada da shugabar kungiyar tarayyar Turai EU Ursula von del Leyen, firaministan Belgium Alexander de Croo, Sai firaministar Italiya kuma mai rikon mukamin shugabancin kasashen G7 Giogia Meloni.