SiyasaTurai
Sarki Charles na Burtaniya zai yi jawabi kan lafiyarsa
December 12, 2025
Talla
Sarki Charles na Burtaniya da ke fama da cutar sankara, zai gabatar da jawabi ga al'umma a wannan Juma'a kan halin da yake ciki, wanda za a yada da karfe 8:00 na dare agogon GMT.
A cikin watan Fabarairun 2024 aka gano Sarki Charles na III na dauke da cutar ta sankara, wadda har yanzu ba a bayyana nau'inta ba ga jama'a, bayan da aka yi masa aikin mafitsara.
Karin bayani:Sarki Charles na Burtaniya ya gayyaci shugaban Amurka Trump
A cikin watan Afirilun 2025 Sarkin ya koma fagen harkokin gudanarwarsa gadan-gadan, bayan dakatarwa na tsawon makonni domin jinyar lalurar da ke damunsa.