Sarkin Ingila King Charles na III ya fara ziyarar a Kenya inda zai fuskanci kiran neman afuwa kan abin da turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka aikata a kasar.
Talla
Ko da yake ziyarar ta kwanaki hudu da sarkin zai kai tare da mai dakinsa Sarauniya Camilla an tsara a matsayin wata dama ta hangen gaba da kuma karfafa dangantaka tsakanin London da Nairobi, har yanzu tabon turawan mulkin mallakar na Burtaniya bai warke ba a zukatan 'yan Kenya.
Wannan dai ita ce ziyarar farko da sarkin mai shekaru 74 a duniya zai kai nahiyar Afirka tun bayan da ya hau gadon sarauta a watan Satumbar bara bayan rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Eliizabeth ta II.
Bikin nadin Sarki Charles cikin hotuna
A Birtaniya an yi bikin nadin Sarauta na farko cikin kusan shekaru 70, irin wanda aka saba a daruruwan shekarun da suka gabata.
Hoto: Dan Charity/AP/picture alliance
A hukumance
Charles ya saka Kambun Sarauta a Mujama'ar St Edward karkashin jagorancin Archbishop na Canterbury, inda ya zauna kan kujera mai shekaru 700.
An shafe fiye da shekaru 1000 ana irin wannan bikin na kasaita a Masarautar Birtaniya. Shi dai Charles na III da ke da shekaru 74 a duniya, ya kasance sarki na 40 da ya rike wanann masarauta kana shi ne mafi tsufa da ya dare kan karagar.
Hoto: Jonathan Brady/PA/REUTERS
Kambun Sarauta
Kambun Sarautar da ya kunshi zinare wanda aka saka wa Sarki Charles na III, an yi shi tun shekarar 1661. Akwai duwatsu masu daraja fiye da 400 a jikin Kambun, wanda sabon sarkin ya saka.
Hoto: Kirsty Wigglesworth/REUTERS
Karagar sarauta
Karagar sarautar na kunshe da duwatsu masu daraja da suka yi karanci, ana ajiye ta a Scotland. A kai ake nada sarakunan Scotland.
Hoto: Kirsty O'Connor/PA Wire/picture alliance
Harabar wajen bikin
Westminster Abbey, ta kasance Cocin da ake nadin Sarauta tun shekarar 1066. Fiye da baki 2,000 aka gayyata wajen nadin Sarki Charles na III a matsayin sabon sarki.
Hoto: Gareth Cattermole/Getty Images
Sarauniya
Za a kira matar Sarki Charles na III da sunan Sarauniya Camilla a hukumance. Wannan mukamin bai sauya ba, cikin shekarun da suka gabata. Amma wasu na kiran Camilla a matsayin daya matar, saboda matar sarkin ta farko ita ce marigayiya Gimbiya Diana. Sai dai ita Camilla ta saka Kambun Sarauta wanda bai janyo cece-kuce ba.
Hoto: Gareth Cattermole/REUTERS
Barandar Fadar Buckingham
Sabon sarki da sarauniya sun koma Fadar Buckingham bayan bikin nadin Sarautar, inda suka bayyana a saman barandar fadar da sauran 'yan gidan sarautar domin gaisuwa ga dubban mutane. Yarima Andrew kani ga Sarki Charles na III da Yarima Harry karamin dan sabon sarkin, ba sa cikin wadanda suka tsaya a barandar.
Hoto: Leon Neal/AP Photo/picture alliance
Tsatson Sarauta
Yarima William wanda yake kan layin zama sarki na gaba, ya sumbaci mahaifinsa tare da durkusa a gabansa domin yin mubaya'a. William yana da yara uku, wadanda sune na biyu da na uku da kuma na hudu a layin gadon sarautar.
Hoto: Yui Mok/AP Photo/picture alliance
Wakili na wucin gadi
Kanin Yarima William wato Harry ya iso wajen bikin shi kadai, maimakon yadda ya saba zuwa tare da matarsa Meghan da ke takun saka da jaridun Birtaniya. Ba ta zo ba saboda ta tsaya agidansu na California a Amirka, domin bikin zagayowar ranar haihuwar dansu na farko Archie da ya cika shekaru hudu a ranar. Harry ya tsaya lokacin da Sarki Charles na III da sauran 'yan Sarauta suka yi faretin sojoji.
Hoto: Andy Stenning/REUTERS
Dan Uwa
An mayar da Yarima Andrew kani ga Sarki Charles na III gefe guda, tun lokacin da aka samu abokinsa Jeffrey Epstein da laifin mai dangantaka da lalata. Mai shekaru 63 a duniya shi ma an zarge shi da lalata, abin da aka sasanta a wajen kotu. Mutane sun yi wa Andrew ihu lokacin da yake wucewa.
Hoto: Roland Hoskins/AP/picture allaince
Manya
Liz Truss ta kasance firaminista ta karshe lokacin Marigayiya Sarauniya Elizabeth kana ta farko lokacin Sarki Charles na III, kuma tana cikin wadanda suka halarci bikin. Boris Johnson kuwa shi ne firaministan da ya ajiye mukaminsa a makonnin karshe na Sarauniya Elizabeth ta II.
Hoto: Gareth Cattermole/AP Photo/picture alliance
Magoya baya
Dubban mutane sun halarci bikin domin taya Charles murna, inda wasu masu goyon bayan Sarauta suka kafa sansani na kwanaki domin ganin komai kai tsaye. Mutane suna taken "Allah taimaki sarki" sannan suna rike da tutocin kasar, akwai kuma kimanin sojoji 7,000 a fadar Buckingham.
Hoto: Bruce Adams/AP Photo/picture alliance
Masu adawa da tsrain Sarauta
Ba kowa yake goyon bayan tsarin Sarauta a Birtaniya ba. Akwai masu adawa da tsarin da suke taken neman soke shi. Suna neman ganin samun tsarin zaben shugaban kasa maimakon amfani da tsarin Sarauta.
Hoto: Piroschka van de Wouw/AP/picture alliance
'Yan Sanda
'Yan sandan birnin London sun kama masu zanga-zanga da dama, inda daruruwan mutane suka fito da rubuce-rubuce lokacin bikin na ranar Lahadi. Gwamnatin Birtaniya tun farkon mako, ta kafa sabuwar dokar hana zanga-zanga.
Hoto: Scot Garfitt/AP Photo/picture alliance
Hotuna 131 | 13
Ziyarar dai na zuwa ne yayin da kasar ta Kenya da ke gabashin Afirka ke shirin cika shekaru 60 da samun yancin kai a watan Disamba mai zuwa. Tun da farko a cikin wannan shekarar Sarkin ya kai ziyara kasashen Jamus da Faransa.
Wata dokar ta baci da hukumomin mulkin mallakar suka kafa a tsakanin shekarun 1952 zuwa 1960 sakamakon boren Mau Mau da suka yi adawa da mulkin mallaka na Burtaniya ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla fiye da10,000 yawancin su 'yan kabilar Kikuyu ko da ya ke wasu manazarta da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce adadin ya fi haka.