1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Salman ya ki halartar taro da Obama

Suleiman BabayoMay 14, 2015

Shugaba Obama na Amirka na taron da takwarorinsa na yankin Gulf . Sai dai sarkin Saudiyya Salman ya ki halarta domin nuna rashin jin dadi kan yarjejeniyar nukiliyar Iran

Hoto: Reuters/K. Lamarque

Taron na wannan mako da ke gudana a wajen hutawar shugaban Amikra da ke Camp David, zai zama dama ga shugabannin kasashen Laraba na yankin tekun Gulf su gana da Shugaba Barack Obama na kasar ta Amirka. Sai dai kafin fara taron Sarki Salman bin Abdul-Aziz Al Saud na kasar Saudiyya ya sanar da cewa ba zai halarta ba, abin da ake gani ya na da nasaba da yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla kan nukiliyar kasar Iran. Kasar ta Saudiyya ta kasance mai adawa da Iran, inda suke tserereniya kan samun karfin fada aji tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Bayan sarkin Saudiyya da ya kauracewa taron, su ma shugabannin kasashen Oman, da Bahran gami da hadaddiyar Daular Larabawa duk sun tura mataimakansu ne. Michael Doran masani a wata cibiyar bincike da ke birnin Washington na kasar Amirka, ya ce babbar manufar Amirka ita ce babu makiyi na har abada.

Shugaban Iran na shirin bayar da Kai game da rikicin nukiliyaHoto: Mehr

Ya ce "A gaba daya manufar ita ce ba wai shawo kan kasashen Labarawa ba ne su amince da yarjejeniya, amma sai domin nuna wa Amirkawa da suke suka cewa za a iya hada hannu da kasashen da ake dasawa da su. A kan haka ya mayar da hankali kan majalisa domin samun kuri'un da za su hana toshe yarjejeniya da Iran."

Akwai masu ganin cewa Sarki Salman bin Abdul-Aziz Al Saud na kasar Saudiyya ya kauracewa taron ne saboda rashin karfin gwiwa da yake da shi a kan gwamnatin Shugaba Barack Obama na kasar Amirka. Amma ba kamar firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ba, kasar Saudiyya ta kauracewa fito-na-fito a bayyane da kasar ta Amirka kan batun nukiliyar kasar ta Iran. Lamarin na Iran ta mayar da manyan batutuwa kamar tsagerun kungiyar IS masu neman kafa daular Islama sun koma kasa a cikin abubuwan da suke daukar hankali.

Michael Doran masani ya nunar da cewa Shugaba Obama ya na da damar samun nasara kan yarjejeniyar ta Iran duk da halin da ake ciki, inda ya ce:" ya na da kyakkyawar damar samun nasara, saboda ba ya bukatar abubuwa masu yawa domin yin nasarar"

Akwai rikice-rikice masu yawa da suke daukar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya kama daga Yemen zuwa kasashen Iraki da Siriya da ake samun masu kaifin kishin addinin Islama. Wasu kasashen na daukan yarjejeniyar nukiliya da Iran a matsayin yadda karfin Amirka ke gushewa a yakin. Sai dai Michael Doran ya na ganin Shugaba Obama zai ci gaba da kasancewa mai shiga tsakani a rikice-rikicen yankin, in da ya ce: "Ina tsammani ya na neman saka Amirka ta zama babbar mai shiga tsakani a yankin."

Sarkin Salman na Saudiyya na so a yi watsi da yarjejeniya da IranHoto: Reuters/A. Harnik

Duk yadda ta kasance Shugaba Barack Obama zai ci gaba da fuskantar kalubale daga sassa daban-daban bisa yunkurin sake mayar da Iran cikin sauran kasashen duniya.