Beljium: Takaicin azabtarwa mulkin mallaka
June 30, 2020Talla
A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Felix Tshisekedi, Sarki Philippe na Belgium ya nuna matukar takaici da cin zarafi da azabtarwa da Belgium ta aikata wa jama'a a Kwango, sai dai bai nemi afuwa ba a hukumance.
An wallafa wasikar a wannan rana da kasar ta Kwango ke bikin cika shekaru 60 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Sarki Philippe ya baiyana fatan kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen biyu ba tare da nuna wariya ba. Ya kuma ce domin karfafa dangantakar da ke tsakaninsu, wajibi ne su gayawa juna gaskiya game da abubuwan da suka faru a baya.