Sarkin Kuwait ya rusa majalisar dokokin kasar
May 11, 2024
Sakin Kowet Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah ya rusa majalisar dokokin kasar a ranar Juma'a tare da daukar nauyin wasu ayyukan gwamnati, makwannin shida kacal bayan zaben da aka gudanar a daular mai arzikin man fetur da ke yankin Gulf.
Karin bayani: Zaben 'yan majalisa a masarautar Kuwaiti
Kamfanin dillanci labaran Kuwait na Kuna ya ruwaito cewa matakin wanda ya jibanci soke wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulki na tsawon shekaru hudu ya biyo bayan rikice-rikicen siyasa da suka kunno kai a kasar a baya-bayan nan.
Kamfanin na Kuna ya kuma kara da cewa sarki Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah da majalisar ministocin kasar za su ci gaba da tafiyar da ayyukan 'yan majalisun domin kawo karshen tarnakin da wannan dambarwa ta siyasa ta kawo wajen gudanarwar hukumomi.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai sabuwar majalisar ta Kowet da aka zaba a farkon watan Afrilu ya kamata ta gudanar da zamanta na farko sa dai amma da dama daga cikin wakilan suka kaurarewa halartar wannan zama domin kin shiga gwamnati.