1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

150911 Libyen Frankreich Großbritannien

September 15, 2011

Nikola Sarkozy da David Cameron sun tattana game da makomar Libiya da hukumomin kasar a birnin Tripoli

Ziyara Sarkozy da Cameron a LibiyaHoto: dapd

Shugaban kasar Faransa Nikola Sarkozy da Firaministan Birnatiya David Cameron, su ka fara wata ziyara aiki ta ba zata a kasar Libiya kwanaki kalilan bayan kifar da shugaba Mohamar Kaddafi.

Da sanhin sahiyar Alhamis ne jiragin dake dauke da Nikolas Sarkozy da David Cameron suka sauka a filin saukar jiragen sama na birnin Tiipoli, inda magabatan biyu su ka samu tarbe kyakkyawa.

A jajibirin wannan ziyara dake wakana cikin tsatsauran matakan tsaro, saida Faransa ta tura kurrarun `yan sanda 160 a birnin Tripoli, domin taimakawa sojojin Libiya kula da lafiyar bakin.

Kasar Faransa na daga sahun gaba na kasashen da su ka yi ruwa su ka yi tsaki domin NATO ta aika sojoji a Libiya da zumar taimakawa yan tawaye su hambara da shugaba Mohamar Khadafi.

A jawabin da yayi Sarkozy ya bayana gamsuwa da rawar da Faransa ta taka a cikin yakinan Libiya ya kara da cewa:

"Mun ceci rayuka dubban jama´a, saboda hake ne ba mu tsaya bata lokaci ba, wajen yanke shawara kai dauki ga kasar Libiya, kuma babu wanda ya soki wannan mataki da mu ka dauka".

An kwashe watani shida a na fafatawa tsakanin dakarun NATO masu tallafawa yan tawayen Libiya da kuma sojoji masu biyyaya ga Mohamar Khaddafi, amma Faransa ba ta yi kasa a gwiwa ba na cimma burin da ta sa gaba.

Kamar yadda shugaban na Faransa ya bayyana lokacin taron kasa da kasa game da Libiya da ya gudana birnin Paris, matakin da Faransa ta dauka na hana dakarun Khadafi kai harin ta sarrain samaniya a birnin Bengazi na daga ababen da suka yi matukar taimakawa yan tawayen:

"Ya ce tun tunni mu ka hana kai hare-hare ta sararin samaniya kan birnin".

Albarkacin wannan ziyara ta yau Nikolas Sarkozy da David Cameron sun ziyarci babbar asibitin Libiya inda su ka gana da mutanen da su ka ji raunuka lokacin yakin.

A yayin da su ka gana da shugaban rikwan kwarya na kasar Libiya Mustafa Abdeljalil, magabatan biyu sun yi alkwarin ci gaba da taimakawa komitin koli na rikwan kwarya har lokacin da kasar Libiya ta zama da gidinta.Sannan sun yi kira ga kasashen duniya mussamman wanda mukkaraban Khaddafi su ka fake a cikinsu su mika su ga kotin kasa da kasa,wadda tuni ta bada sammacin su.

Nikolas Sarkozy ya yi amfani da wannan dama inda ya mussanta zargin da ake yi wa kasarsa na cewar ta cimma wata yarjejeniyar sirri da sabin magabatan Libiya, game da ganimar man fetur.

Bayan Tripoli Sarkozy da Cameron za su ziyarci birnin Benghazi, inda za su gabatar da jawabin a wani fili na mussamman da a ka radawa suna dandanlin kwatar yanci.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal