Sarkozy ya yi gargadin kai harin 'yan ta'adda
October 14, 2016Talla
Tsohon shugaban ya ce ba magana ba ce ta idan za a kai hari ba, a a yau she ne za a kai shi, wannan ne abin tambaya.
Sarkozy ya bayyana haka ne a muhawara da suka yi da sauran 'yan siyasa shida da ke neman tsayawa jam'iyyar 'yan Conservative masu ra'ayin mazan jiya a zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Sarkozy da abokin karawarsa Alain Juppe sun maida hankali kan batun yaki da ta'addanci a muhawarar inda Sarkozy ke neman a kai ga garkame wadanda ke zama babar barazana cikin wadanda ya kira "Masu tsatstsauran kishin addinin Islama". Juppe na kafewa a kan cewa alkali shi ke da tacewa.
Za dai a yi zaben fidda gwani na masu ra'ayin mazan jiya a ranakun 20 da 27 ga watan Nuwamba mai zuwa.