Sarrafa hikimomi ta hanyar amfani da hasken rana
February 24, 2016Wannan tunanin dai ya fara zuwa daga Yecheou Abdou, shi da sauran abokanan sa un samar da wata kungiya don tafiyar da harkokin kasuwancin nasu. A yankunan karkara dai mata ne ke yin sissika domin samar da kwayoyin dawa da gero da sauran su wajen yin amfani da hannayen su da ko kuma injina masu amfani da man Diesel. To amma yanzu abin ya sauya, Yecheou Abdou tuni ya sayar da injina hudu ga mutanen yankin su, kowanne inji ya kan tashi akan Euro 480.
"Injin yana amfani da hasken rana ne wato Solar, babu bukatar tattara makamashin ba kuma bukatar man Diesel. Inji daya na iya wadatar da kauye guda da ke da mutane har dubu guda."
Yecheou Abdou na samun tallafin wata cibiya mai suna Cipmen a Niamey a inda matasa masu harkokin kasuwancin kan saduwa don yin aiki tare na samar da fasahar saukaka harkokin sufuri ko kuma wasu sabbin bayanai kan makamashi. Har yanzu dai Jamhuriyar Niger ba ta yi suna ba wajen kasancewa depo a harkar irin abubuwan da kamfanin ke samarwa. Almoukhar Alahoury shi ne babban darektan kamafanin ya kuma yi karin haske kan kamfanin.
"Dabi'ar kasuwanci bata watsu sosai ba a cikin al'ummar mu ,mafi yawancin mutane na aiki ne da bangarorin da ba a karkashin gwamnati ba, to amma yanzu muna kokari ta yin amfani da irin wadannan cibiyoyin kana kuma mu na da damar kawo sauyi kan hakan."
Mutane da yawa a Niger na samun kudade ne ta hanyar yin kananan ayyuka, amma ga wanda zai fara kafa kamafani yana da wuya ya samu tallafin bashi daga banki don haka cibiyar Cipmen ta shigo don tallafawa.
"Muna tantance mutane da yawa da za su tallafawa kananan masana'antu wajen aiwatar da manufofin su. Misali mun samar da wata alaka da minista ko wata cibiya ta kasa da kasa kana a bangaren masu zaman kansu mun bude kofofi ta yadda za su fara kasuwanci."
Lallai kasuwar ba laifi, inji Yecheou Abdou tsakanin lokacin da na fara harkokin kasuwancin nan zuwa yanzu, kasuwancin ya bunkasa sosai, kuma mutane da dama sun tittido don ganewa idanuwan su yadda harkar take. Masa'na'antar dai yanzu haka ta dauki ma'aikata biyar wadanda ke kai wa tare da harhada faya fayen solar a kauyukan kasar ta Niger baki daya.