An rarraba jami'an jinya fadin kasar Afirka ta Kudu
April 24, 2020Talla
Shugaban ya kara da cewar wannan sanarwa ba ta shafi iyakokin kasar ba wadanda za su cigaba da zama a rufe sannan haramcin sayar da barasa na nan har yanzu. Da suke bayyana ra'ayoyinsu game da wannan daukar mataki, shugabannin jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance wato DA sun jinjinawa shugaba Ramaphosa da kuma bayyana shi a matsayin zakaran gwajin dafi a wannan lokaci da annobar COVID-19 ta jefa iyalai da sana'o'i cikin mawuyacin hali.
A nasa bangaren ministan lafiya a kasar ta Afirka ta Kudu Zweli Mkhize ya shaidawa manema labarai cewar an rarraba ma'aikatan jinya da yawansu yaki dubu 28 sassa daban-daban na kasar domin aikin gwajin cutar ta Coronavirus.