SiyasaGabas ta Tsakiya
Saudiyya ta kakkabo makamai masu linzami daga mayakan Houthi
September 24, 2026
Talla
Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar tsaron fararen hula ta Saudiyya ta fitar da jerin gargadi a birnin Makka da wasu yankuna, kan yiwuwar barazanar makami mai linzami ko jirgi mara matuki.
Matakin ya zo ne bayan da Saudiyya ta zargi kungiyar Houthimai samun goyon bayan Iran da kai harin jirgi mara matuki kan Makka a makon da ya gabata, zargin da kungiyar ta musanta.
Kwanaki kadan bayan haka, kungiyar Houthi ta kai hari kan birnin Riyadh, lamarin da ya kara tsananta rikicin da ke tsakanin kungiyar da Saudiyya.
Kungiyar ta kuma kwace wasu yankunan bakin teku masu muhimmanci kusa da mashigin Bab al-Mandab, hanyar da Saudiyya ke amfani da ita wajen jigilar man fetur, lamarin da ke kara jefa yakin Yemen cikin rikicin Gabas ta Tsakiya.