Saudiya ta karyata ikirarin Isra'ila na shiga kasar
January 27, 2020Talla
Dokar na nan daram inji mahukunta Saudiya saboda haka duk mai dauke da fasfon kasar ba zai sanya kafarsa a kasa mai tsarki ba. A jiya Lahadi ne ma'aikatar harkokin cikin gidan Isra'ilan, ta fidda sanarwar, inda a ciki ta ce an amince da bai wa 'yan kasar izinin shiga Saudiyya, walau don ibada ko hada-hadar kasuwanci na wani takaitaccen lokaci.
Yanzu dai an kasa kunnuwa don jin sakamakon bayanan da Shugaban Amurka Donald Trump zai yi a game da shirin samar da zaman lafiya a tsakanin Yahudawa da Falisdinawa a wannan Litinin, kafin a kai ga fahimtar yadda dangantaka a tsakanin Isra'ila da sauran kasashen musulmi za ta kasance.