Amirka da Saudiya na zargin Iran
September 18, 2019Tsamin dangantakar ya karu ne bayan harin da Saudiyya da Amirka ke cewa suna da yakinin Iran ce ta kai shi, inda ma sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka Mike Pompeo zai gana da yarima mai jiran gado na Saudiyan Mohammed bin Salman domin tattauna irin matakin da ya kamata su dauka kan harin. Sai dai a wata takarda da ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Iran ta aikawa da Amirkan ta hannun ofishin jakadancin kasar Switzerland da ke Tehran fadar gwamnatin kasar, ta nunar da cewa ba ta da wata alaka ta kusa ko ta nesa da harin. Daga cikin wani bangare na takaddar da kamfanin dillancin labarai na kasar Iran din IRNA ya wallafa, Tehran din ta ce in har aka dauki wani mataki a kanta dangane da wannan batu, to kuwa za ta mayar da martani nan take. Tuni dai Shugaba Donald Trump na Amirkan ya bayar da umarnin kara kakabawa Iran din sababbin takunkuman karya tattalin arziki.