060611 Saudi-Arabien Spurensuche
August 8, 2011Ƙasar Amirka na ɗaukar Saudiyya a matsayin abokiyar aiki a fannin dabarun tsaro. To amma wannan ƙawance ya shiga wani hali na rashin fahimta tun bayan harin 11 ga watan Satumba bayan da aka gano cewa mafi yawan waɗanda suka aiwatar da hare haren sun fito ne daga ƙasar Saudiyya. Bugu da ƙari bakin ƙwararrru ya zo ɗaya da cewa mafi yawan kuɗaɗen tallafi da ƙungiyar al-Ƙa'ida ke samu har i yau suna fitowa ne daga Saudiyyar da sauran ƙasashen yankin Gulf.
A lokacin da shugaba Barack Obama na Amirka ya kai ziyara a birnin Riyad na ƙasar Saudiya a matsayin ɓangare na rangadin da yayi a Gabas ta Tsakiya a watan Yunin shekarar 2009 bai yi wata wata ba wajen jinjina wa gidan sarautar wannan daular inda ya ce ƙasashen biyu abokan aiki ne a fannin dabarun tsaro ya kuma yaba ma Sarki Abdullah bisa hikimarsa da kuma halinsa na dattako.
Ƙawa mai fuskoki guda biyu
To amma saɓanin haka an samu wasu bayanan sirri da shafin yanar gizo na Wikileaks ya buga da suka rawaito sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton na mai zargin ƙasar ta Saudiyya da cewa:
"Babban ƙalubale da har yanzu ake cigaba da fuskanta shine na shawo kan Saudiyyar a hukumance da ta tinkari matsalar samar da kuɗaɗen tallafa wa 'yan ta'adda daga cikin gidanta a matsayin muhimmiyar dabara ta aikin tsaro."
Wannan kalaman dai na bayyana haƙiƙanin take-take masu sarƙaƙƙiya na wadannan ƙasashe guda biyu. A ɓangare guda ba ma Saudiyya tana zaman muhimmiyar abokiyar cinikin Amirka wajen samar mata da man fetur kaɗai ba ne a'a Fadar White House tana kuma ɗaukar Saudiyya a matsayin muhimmiyar ƙasa wajen murƙushe ƙarin angizo da Iran ke samu a wannan yanki da kuma matsayinta na bin hanyoyin diplomasiya wajen warware rikicin wannan yanki.
A ɗaya ɓangaren kuma Saudiya tana cigaba da aikata dangogin ta'asar da Amirka ke sukan wasu ƙasashe da aikata su. Waɗannan laifuka sun haɗa ne da cin zarfin bil Adama da rashin tabbatar da 'yancin addini da kuma haramci akan wasu fasahohin aikin magani sannan uwa uba fifita mata akan maza, waɗanda mafi yawansu suka haifu daga matsananciyar aƙidar nan ta Wahabiyanci. Guido Steinberg ƙwararren masani akan ta'addanci da matsanancin ra'ayi na Islama na gidauniyar nazarin kimiyar siyasa dake birnin Berlin na nan Jamus ya ce akwai alaƙa tsakanin aƙidar Wahabiyanci da aƙidar ƙungiyar al-Ƙa'ida.
Tallafa wa ayyukan masu matsanancin ra'ayi
"Dalili kenan da ya sa a ko da yaushe matasa ke watsa matsanancin ra'ayi na Islama bisa abin da aka koyar da su a makarantu da jami'o'in Saudiyya. To amma shugabannin Saudiyya ba su son rabuwa da wannan aƙidar dake da alaƙa da manufar gwamnati da kuma aƙidar al-Ƙa'ida."
Sukan da ake wa Saudiyya bisa tallafa wa ayyukan tarzoma ya ma fito fili ne bayan da shafin yanar gizo na Wikileaks ya buga bayanai na musamman dake nuni da cewa mafi yawan kuɗin dake faɗawa hannun 'yan al-Ƙa'ida yana fitowa ne daga ɗaiɗaikun mutane daga ƙasashen Gulf. Yassin Musharbash ma'aikacin mujallar Der Speigel ta nan Jamus ya ce akwai shaidar dake tabbatar da hakan.
"Tun daga lokacin da 'yan Mujahidin na ƙasar Afganistan suka gwabza yaƙi da Tarayyar Sobiet ne dai Larabwan yankin Gulf ke taimaka musu da kuɗi. Su dai Larabawan yankin Gulf suna ba da tallafin kuɗin ne domin nuna goyon bayansu ga wannan al'amari. Akwai ma wasu daga cikinsu waɗanda daga bisani suka cigaba da tura nasu taimakon."
Ra'ayin ƙawararrun masanan dai ya zo ɗaya da cewa hakan ya wakana tsakanin ƙasar Saudiyya da sauran ƙasahen yankin Gulf ne bisa matsayin da suka ɗauka a wancan lokaci. Bayan harin 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 ne kuma mahukunta suka rufe gidauniyar Alharamain saboda cewa daga gareta ne ƙungiyoyin 'yan bindiga da na 'yan ta'adda ke samun tallafin kuɗi kai tsaye a cewar Guido Steinberg. Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2003 ne kuma gwamnatin Saudiyya ta tsaurara matakan sa ido domin zaƙulo 'yan ta'adda bisa matsin lambar Amirka.
Mawallafa: Khalid El Kaoutit / Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal