Mace ta zama jakadiyar Saudiyya a Amirka
February 24, 2019Kasar Saudiyya ta nada mace a matsayin jakadarta a kasar Amirka, a daidai lokacin da huldar Saudiyyar da hukumomin Amirka ke cikin wani yanayi na tangal-tangal sakamakon kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya.
Wannan dai shi ne karon farko a tarihin diflomasiyyar Saudiyyar, da Rima bint Bandar wadda 'ya ce ga arima Bandar bin Sultan za ta rike mukamin mai matukar kima, inda ta canji kanin Yarima Muhamed bin Salman wato Khaled bin Salmane, wanda shi kuma aka nada shi a matsayin karamin ministan harkokin tsaron Saudiyya.
Masana dai na kallon nadin mukamin da hukumomin na birnin Riyadh suka yi, baya rasa nasaba da neman sake maido da kimar Saudiyya ga Amirka, wacce ta gurbace tun bayan kisan Kashoggi, da kasar Amirkan ke zargin Yarima Salman da hannu a ciki, zargin da kuma kasar Saudiyya ta sha musantawa.