1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Bincike game da kisan Khashoggi

Abdullahi Tanko Bala
November 12, 2018

Birtaniya ta bukaci Saudiyya ta bada cikakken hadin kai game da binciken da ake yi kan kisan dan Jarida Jamal Khashoggi

Portraitfoto: Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/AP/A. Nabil

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt a yau Litinin zai kai ziyara Saudiyya domin tattaunawa da kuma yin matsin lamba ga yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman dangane da kisan gillar da aka yiwa dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

A yayin ziyarar wadda za ta kai shi zuwa kasar hadaddiyar daular larabawa, Hunt zai kuma bukaci karin goyon baya ga yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na kawo karshen yakin da ake yi a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ruwaito cewa Yarima Mohammed Bin Salman ya tattauna ta wayar tarho da Simon McDonald jakadan musamman na Firaministar Birtaniya Theresa May game da dangantaka tsakanin Saudiyya da Birtaniya.

Birtaniya dai na bukatar Saudiyya ta bada cikakken hadin kai ga binciken da ake yi kan kisan Jamal Khashoggi.