Saudiyya da Rasha na fatan karfafa dangantaka
October 5, 2017Talla
Ziyarar wadda ke zama ta farko da sarki Salman ya kai Rasha na da nufin kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Putin da sarki Salman sun tattauna kan batutuwan da suka hada da kasuwar mai a duniya da kuma yakin Siriya.
Sau da dama dai dangantaka tsakanin kasashen biyu ta na tsami a baya.
A lokacin yakin cacar baka Saudiyya ta taimaka wajen baiwa 'yan tawayen Afghanistan makamai a yaki da tarayyar Soviet.
A baya bayan nan kuma tsamin dangatakar ta yi kamari kan yakin Siriya inda Rasha ta mara baya ga shugaba Bashar al Assad yayin da Saudiyya kuma ta goyi bayan masu adawa da shi.
Ana sa ran bangarorin biyu za baiyana kulla harkar kasuwanci ta miliyoyin daloli.