1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Mace ta farko 'yar sama jannati

May 22, 2023

Wani kumbo na kamfanin Amurka da ake kira Axiom Space ya tashi zuwa cibiyar bincike ta sararin samaniya dauke da masana kimiyya hudu ciki har da wata mace 'yar kasar Saudiyya.

SpaceX Axiom Mission 2
Hoto: Saudi Press Agency/REUTERS

Rayyana Barnawi ita ce mace ta farko 'ya kasar Saudiyya da ta fara irin wannan balaguro na zuwa sararin samaniya kuma tare da abokan aikinta hudu za su gudanar da bincike-bincike akalla 20 a tsawon lokacin da za su share a cibiyar NASA.

Kafin tashin kunbon mai lakabin Dragon, Rayyana Barnawi masaniya a fannin kimiyya ta bayyana wa manema labarai farin cikinta na kasancewa mace 'yar kasar Saudiyya ta farko kuma mace ta farko a yankin kasashen larabawa da za ta taka duniyar sararin samaniya.

Ko baya ga Rayyana Barnawi akwai kuma wani mutum guda shi ma dan kasar Saudiyya da ke cikin tawagar 'yan sama Jannatin hudu da suka tashi zuwa sararin samaniya.