1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta amince da halaccin kasar Isra'ila

Mahmud Yaya Azare RGB
April 3, 2018

Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman, ya amince da halaccin kasar Isra'ila, a daidai lokacin da Falasdinawa ke kara matsa kaimi don ganin sun 'yanto yankunansu da Isra'ilan ta mamaye.

Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Bayan shekarun da Sarakunan Saudiyya da suka gabata suka kwashe suna daukar Isra'ila a matsayin babbar abokiyar gaba, Yarima mai jiran gado a Saudiyya bin Salman ya amince da hakkin Isra'ila na samun kafuwar kasarta mai cikakkiyar 'yanci, kamar yadda ya fadi a wata  hirar da ya yi da mujallar The Atlantic ta Amirka, batun da tuni ya haifar da cece-kuce.

 Ali Fidhalah, wani fitaccen marubuci a Saudiyya ya ce lokaci ya yi da kasar za ta dawo daga rakiyar gidadancin da ta jima tana yi. 

"Isra'ila kasar ce da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da halaccinta, ana ta hulda da ita. Rashin lissafi ne mu ce za mu ci gaba da yanke alaka da ita, tun da yin hakan ba zai cutar da ita ba ko kadan. Me zai hana mu kulla alakar cudeni in cudeka da ita, don cin moriyar juna?"

 Abdul-Azezz Al-qinae, malami a jami'ar King Fahad, siffanta furucin Yariman ya yi da gagarumar jarumta. 

"Abun takaici kasashe da dama na fakewa guzuma su harbi karsana dangane da rikicin Falasdinawa da Isra'ila. A kan wannan batun Saddam ya mamaye Kuwait. Da haka kuma Iran da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda ke fakewa suna tayar da tarzoma a yankunanmu. Idan Saudiyya ta jagoranci Larabawa kulla alaka da Isra'ila, hanzarin Isra'ila ya kare na ci gaba da mamaye yankunan Falisdinawa, don sun riga sun zama kawaye.”

Shi kuwa Naseer Al-Duwailat, wani dan adawa a kasar ta Saudiyya, gargadin Yariman ya yi da ya yi hattara kar amar sakiyar da ba ruwa.

"Isra'ila za ta ci gaba da keta hurumin kasar Saudiyya, idan har muka ba ta kai bori ya hau. Za ta zama jagora a yankin, za ta yi ta dasa miyagu da 'yan  leken asiri  a cikinmu, don lalata tarbiyya da durkusar da tattalin arzikinmu."

Idan ana iya tunawa, a shekarar 2002 Saudiyya ta yi wa Isra'ila tayin ta janye daga yankunan Falisdinawa, ita kuma za ta gamsar da sauran Larabawa su amince da halaccinta, amma Isra'ilan ta yi fatali da wannan tayin.