Saudiyya ta ba da izinin bude gidajen sinema
December 11, 2017Mahukuntan kasar Saudiyya sun ba da izinin sake bude gidajen sinema da wasu wuraren shakatawa da nishadantarwa a kasar bayan shekaru 35 na haramci. Ofishin ministan raya al'adun kasar ta Saudiyya ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce matakin zai soma aiki a farkon shekara ta 2018, amma tun yanzu gwamnatin za ta soma bayar da lasi ga masu bukatar bude gidajen sinemar.
Gwamnatin kasar ta Saudiyya na son yin amfani da sabon salon mulkin da yarima Mohammed Ben Salmane ya kaddamar domin farfado da matakan raya al'adu ta hanyar bude gidajen shakatawa na kade-kade da wake-wake da na wasanni da ma na sinema wannan kuwa duk da adawar da matakin ke fuskanta daga masu ra'ayin rikau a kasar wadanda ke kallon wadannan wurare a matsayin na alfasha.