1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Saudiyya ta bukaci a dakatar da Isra'ila daga shiga Rafah

Binta Aliyu Zurmi
February 10, 2024

Kasar Saudi Arabia ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta dakatar da sojojin Isra'ila daga kai hari garin Rafah da al'ummar Falasdinu ke neman mafaka.

Saudi-Arabien, Riyadh 2024 | Treffen zum israelischen Krieg in Gaza
Hoto: Saudi Press Agency/APA/ZUMA/picture alliance

Mahukunta a Saudiyya sun yi gargadi a kan irin mumuna bala'in da ka iya aukuwa ga cinkoson Falasdinawan da ke neman mafaka a Rafah idan sojojin Isra'ila suka kai farmaki.

Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Saudiyya ta yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya shiga tsakani.

Sanarwar ta kara da cewar akwai bukatar kwamitin ya duba ci gaba da karya dokokin kasa da kasa gami da dokokin jin-kai da dakarun Isra'ila ke yi

Mahukntan na Riyadh dai sun yi Allah wadai da halin da Falasdinawa ke ciki, a daidai lokacin da Firaministan Isra'ila Benjamin Nathenyahu ke ci gaba da kafewa kan matsayarsa ta tura sojoji garin na Rafah da dubban Falasdinawa ke neman mafaka.